Majalisar Wakilai Ta Gayyaci Ministan Harkokin Waje Da NEMA Domin Jin Bahasi Kan Kwaso Yan Najeriya Daga Sudan

0 60

Majalisar wakilai ta tarayya ta gayyaci ministan harkokin waje, da hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje da kuma hukumar agajin gaggawa ta kasa (NEMA) da su bayyana a gabanta domin bayar da bahasi akan halin da ake ciki dangane da kwaso ‘yan Najeriya daga Sudan.
Kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila, ya fadi haka yayin da aka dawo zaman majalisar a Abuja dangane da matsalar da ake fuskanta dangane da kwaso ‘yan Najeriya daga Sudan.
Femi Gbajabiamila yace cikin makonnin kadan da suka gabata jamhuriyar Sudan ta fada yaki, inda ya kara da cewa abin takaici ne yadda rikicin ya rutsa da ‘yan Najeriya da dama wadanda ke zaune a kasar.
Yace ana cigaba da kokarin tabbatar da cewa an kwaso ‘yan Najeriya dake zama a kasar Sudan a matsayin dalibai, da ‘yan kasuwa da sauran masu sauran sana’o’i lami lafiya.
Yace majalisar na sane da wahalhalun da ake sha wajen kokarin kwaso ‘yan Najeriyar da kuma martanin da gwamnatin tarayya ke bayarwa akan abubuwan dake faruwa a jamhuriyar ta Sudan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: