Buhari Ya Tafi Landan Domin Halartar Nadin Sarkin Birtaniya

0 80

A yau ne shugaban kasar zai tafi birnin Landan na kasar Birtaniya domin halartar taron nadin sarautar Charles na 3 da uwargidansa Camilla a matsayin mai martaba sarki da matar sarkin Ingila.

Shugaban kasar zai samu rakiyar sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, da ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, da ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya), da darakta janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa, Ambasada Ahmed Rufa’i Abubakar, da Shugabar Jami’in Hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa da sauran manyan jami’an gwamnati.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina a wata sanarwa da ya fitar a yau ya ce za a yi bikin nadin sarautar ne ranar Asabar. Ya ce gabanin nadin sarautar, sakateriyar kungiyar kasashe renon za ta yi amfani da damar halartar shugabannin kasashen a birnin London domin karbar bakuncin taron koli na shugabannin kasashe da gwamnatocin kasashen kungiyar a ranar Juma’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: