Akwai Yiwuwar Yau Wasu ‘Yan Najeriya da Aka Kwaso Daga Kasar Sudan Su Iso Kasarnan

0 86

Alamu na nuna cewa a yau ne wasu ‘yan Najeriya da aka kwaso daga kasar Sudan da ke fama da rikici za su iso kasarnan.

Gwamnatin tarayya ta ki sanar da ranar isowar mutanen.

Sai dai al’amura a Masar da Port Sudan sun nuna cewa a yau rukunin farko na ‘yan Najeriya za su sauka a Abuja ko Legas a yau.

Mutanen da suka bar birnin Khartoum na kasar Sudan a ranar Larabar da ta gabata kuma suka makale a kan iyakar Masar na tsawon kwanaki shida a karshe sun samu amincewar hukumomin Masar a ranar Litinin domin ci gaba da tafiya.

Sai dai hukumomin Masar za su ba da damar shiga cikin kasarsu ne hakikanin adadin kujerun da ake da su a jirgin sama, kamar yadda yake a yarjejeniyar fahimtar juna da ta kulla da Najeriya.

Sai dai a yayin da ake jiran izinin hukumomin Masar, da yawa daga cikin motocin bas din sun sauke jakankunan daliban inda suka yi tafiyarsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: