‘Yan Najeriya Dubu 13 Ne Suka Ci Gajiyar Tallafin Annobar Ambaliyar Ruwa A Fadin Jihohin Da Abin Ya Shafa

0 107

Gwamnatin tarayya ta ce sama da ‘yan Najeriya dubu 13 ne suka ci gajiyar tallafin annobar ambaliyar ruwa a fadin jihohin da abin ya shafa a kasar.

Babban Sakatare na Ma’aikatar Agaji, Kula da Annoba da Walwalar Jama’a Dakta Nasir Gwarzo ne ya bayyana hakan a jiya.

Ya bayyana haka ne a yayin wani taro da masu ruwa da tsaki a harkokin ayyukan jin kai a Abuja.

Ya ce an zabo wadanda suka ci gajiyar tallafin daga jihohi 16 da iftila’in ambaliyar ruwa na shekarar 2020 ya shafa a kasar.

Ya kara da cewa jihohin sun hada da Jigawa, Bauchi, Katsina, Yobe, Adamawa, Kogi, Benue, Nasarawa, Kwara, Niger, Kebbi, Sokoto, Anambra, Bayelsa, Delta da kuma Rivers.

Ya bayyana kudirin gwamnatin tarayya na bayar da tallafin da ake bukata ga marasa galihu a kasarnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: