

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a jiya ya umarci hukunta wadanda suka shigo da gurbataccen mai cikin kasarnan.
Gwamnatin Tarayya a ranar Talata tace sinadarin methanol da aka samu kwanannan a cikin man fetur din da aka shigo da shi, ya wuce kima.
Lamarin ya jawo karancin man da dogayen layukan ababen hawa a gidajen man manyan birane irinsu Lagos da Abuja.
Gwamnati a ranar Laraba tace an samu karancin mai na kwanaki 10 a guraren adana man fetur na kasa.
A ranar Larabar, gwamnatin tarayya tace zata gudanar da gagarumin bincike domin sanin yadda aka shigo da gurbataccen man fetur cikin kasarnan.
A wata sanarwa da aka fitar a ranar ta laraba da yamma, managing daraktan kamfanin mai na kasa NNPC, Mele Kyari ya lissafa kamfanin MRS da Oando da sauransu a matsayin wadanda suka shigo da gurbataccen man.