Kungiyar Malaman Makaranta ta kasa reshen jihar Jigawa ta kashe kudi miliyan 38 wajen gina sabbin shaguna
Kungiyar Malaman Makaranta ta kasa reshen jihar Jigawa ta kashe kudi fiye da naira miliyan talatin da takwas wajen gina sabbin shaguna da ofis-ofis a Sakatariyar kungiyar dake Dutse.
Shugaban kungiyar Comrade Abdulkadir Yunusa Jigawa ya bayyana haka a jiya lokacin kaddamar da bude sabbin shagunan da ofisoshin.
Ya ce sun tara kudaden da aka gina shaguna da ofisoshin ne da kudaden da ake yanka na wata-wata daga albashin malamai.
Comrade Abdulkadir Yunusa Jigawa ya kara da cewa an gina ofisoshin ne domin shugabannin kungiyar su ji dadin gudanar da ayyukan su, yayin da shagunan kuma za su rika samarwa kungiyar kudaden shiga.
A jawabinsa kwamishinan Ilimi na Jiha Dakta Lawan Yunusa Dan-Zomo da ya samu wakilcin, babban daraktan sashin duba makarantu, Malam Abdullahi Yunusa, ya ce samar da gine-ginen ya nuna a fili yadda ake alkinta kudaden malamai da kungiyar take yanka na wata-wata.