An tabbatar da jihar Gombe na cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a kasar nan

0 92

An tabbatar da jihar Gombe na cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a kasar nan.

An fitar da sanarwar ne a wani rahoto da wata kungiya mai suna Eons dake sa ido ta fitar a jiya.

Rahoton yayi duba ne kan yawan laifuka wanda suka hada da garkuwa da mutane, da kuma wasu laifuka da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane a watan janairu 2022.

Rahoton ya bayyana cewa Jihar Neja tana kao mafi yawa na aikata laifuka a kasar a watan bayan da aka samu laifun garkuwa da mutamne 396 tare mutuwar mutane 26, yayin da jihohin Zamfara da kaduna suka ta biyo bayanta.

Bayanin yazo ne makwanni kadan bayan ansanar da Jihar Gombe a matsayin jihar da tafi zaman lafiya a yankin arewa maso gabas a lokacin taron da masu ruwa da tsaki a kan harkar tsaro sukayi a jihar.

Jihar ta Gombe a halin yanzu ita ce jiha ta daya a saukin gudanar da kasuwanci a Nigeria.

Leave a Reply

%d bloggers like this: