Shugaba Buhari yace dukwani kudi da aka sace domin aikin cigaban yankin Niger Delta zasu kwato su

0 91

Shugaban kasa Muhammadu buhari yace dukwani kudi da aka sace domin aikin cigaban yankin Niger Delta zasu kwato su tare da hukunta dukwanda keda hannu a karkatar da kudaden.

Ya kuma yi takaici akan yanda wasu tsirarin mutane sukaita sace kudaden cigaban yankin sama da shekara 20 da kafa hukumar dake kula da yankin.

Buhari ya bayyana hakan ne a yau Alhamis ta bidiyon kai tsaye, a lokacin dayake kaddamar da wani katafAren Otel a cikin jami’ar Uyo dake Akwa Ibom.

Mai taimakwa shugaban kasa a kafafen yasa labarai Femi Adesina ne ya bayyana hakan cikin wani sako da yamasa take da Bincikar kudin yankin Niger, Kwatowa da kuma Hukuntawa.

Anasa jawabin shugaban kasa Muhammadu buhari yace, rayuwar al’ummar yankin Niger Delta, zata kasance mai kyau, da ace kudaden da ake warewa hukumar sama da shekara 20 ana amfani su ta hanyar data da ce.

Leave a Reply

%d bloggers like this: