Shugaban Kwamatin Yada Labarai na Majalisar Dattawa, kuma Sanatan Jigawa ta Arewa Maso Yamma Sanata Abdullahi Danladi Sankara, ya bada Motoci 12 da kuma Naira Miliyan 2 da Dubu 200 ga Jam’iyar APC ta Jihar nan.

Shugaban Jam’iyar APC na Jihar Jigawa Alhaji Aminu Sani Gumel, shine ya tabbatar da rabon motocin ga manema Labarai a jiya a Dutse, inda ya yabawa Sanata bisa bada motocin.

Alhaji Aminu Sani, ya ce an raba motocin ga shugabannin Jam’iya na Kananan Hukumomi 12 wanda Sanatan ya ke wakilta tare da basu Naira dubu 200,000 ga kowanne Shugaban Jam’iyar domin ya sha mai.

Kazalika, ya ce Jam’iya tana farin ciki da rabon motocin da Sanatan ya yi, inda ya bukaci sauran Sanatoci suyi koyi da shi.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: