Lai Muhammad yace babban kalubalen da gwamnatin Najeriya ta fuskanta a 2021 shine rashin tsaro bana yunwa ba

0 44

Ministan yada labarai da al’adu na kasa Lai Muhammad yace babban kalubalen da gwamnatin tarayya ta fuskanta a 2021 shine rashin tsaro ne.

Ministan ya bayyana hakan ne a yau alhamis, a lokacin dayake zantawa da manema labarai, a yayinda yake bayyana nasarorin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu buhari a wannan shekarar.

A cewarsa gwamnatin shugaba Buhari, bayan tarun nasarori data samu, matsalar tsaro tana ciwa gwamnatin tuwo a kwarya.

Ya kuma kara da cewa jami’an sojin kasar nan sun samu nasarori sosai, wajan kakkabe yan bindiga.

Lai ya kara da cewa gwamnatin nan ta samu nasarar murkushe yan ta’adda 1000, tare da kwato mutane dubu 2 a 2021

Akwai kuma mutane dubu 22 da suka ajiye mukaman su a yankin arewa maso gabas a wannan shekarar.

Tare da kwato makamai da kuma kayan kera bama bamai daga yan ta’adda a fadin kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: