Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kama wasu mutane masu sojan 3 tare da miyagun kwayoyi masu nauyin kilogram 427 a jihar Borno da babban birnin tarayya Abuja.

Daraktan yada labarai na hedikwatar hukumar na kasa dake Abuja Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a yau alhamsi a babban birnin tarayya.

A cewarsa an samu nasara kama daya daga cikin masu laifin, mai suna Yakubu Kotri wanda yayi shigar soji a ranar laraba, yana tuka mota kirar Gulf a Karamar hukumar Bama dake jihar Borno dauke da tabar wiwi mai nauyin kilogram 208.

Sai kuma wani mai suna Salisu Muhammad wanda yake amfani da kayan wani jama’in tsaro, an kuma kama shi ne da Tiramol a Bama dake jihar Borno, sai kuma wani mutum guda aka kama a babban birnin traayya Abuja.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: