

Ana sa ran Shugaban Kasa Muhammadu zai sanya hannu akan kasafin kudin badi a ranar Juma’a mai zuwa, 31 ga watan Disambar da muke ciki.
Hakan ya biyo bayan aikawa da kudirin kasafin kudi da aka sanyawa daga majisun kasa.
Wata majiya a ofishin akawun majalisar kasa ta tabbatar da cewa an aika da kasafin kudin ga shugaban kasar.
Majiyar ta musanta rahoton dake cewa ba a aika da kasafin kudin zuwa ga shugaban kasa ba, kwanaki 3 kafin shekarar ta kare.
Majalisar wakilai da ta dattawa sun zartar da kasafin kudin badi a makon da ya gabata, kafin su tafi hutunsu na shekara-shekara.