Za a sanya takunkumi ga masu wasu gine-gine 435 da ba a kammala su ba a Abuja

0 96

Hukumar babban birnin tarayya Abuja, ta ce an kammala shirye-shiryen sanya takunkumi ga masu wasu gine-gine 435 da ba a kammala su ba, kuma da aka yi watsi da su a babban birnin tarayya Abuja.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan kula da filaye na hukumar, Adamu Hussaini.

Daraktan ya ce an dauki matakin ne domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin da ke da fadin murabba’in kilomita 250 na Abuja.

Adamu Hussaini, wanda ya bayyana cewa matakin na iya hadawa da kwace wasu filaye, ya shawarci masu irin wadannan gine-ginen da aka yi watsi da su da kuma wadanda ba a kammala ba a cikin birnin da su hanzarta yin aiki don kammala wadannan gine-gine.

A cewarsa, irin wadannan gine-ginen sun zama sanadin tabarbarewar tsaro a birnin.

Ya kuma bayyana cewa hakan na iya faruwa ga masu filaye kusan 600 da ba a gina su ba a birnin tarayya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: