An sanar da mutanen jihar Yobe game da shirin tayar da bama-baman da basu fashe ba

0 79

Gwamnatin jihar Yobe ta sanar da al’ummar jihar game da shirin tayar da bama-baman da basu fashe ba, wanda helkwatar sashe na 2 na Operation HADIN KAI na rundunar sojin Najeriya ta shirya a Damaturu.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da aka fitar a yau ta hannun Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam mai ritaya, mai baiwa gwamna Mai-Mala Buni shawara kan harkokin tsaro a Damaturu.

Abdulsalam ya ce za a tayar da bama-baman ne a kusa da jami’ar jihar dake Damaturu a kan titin Gujba da kuma kan titin Maiduguri.

A cewar sanarwar, ana sanar da jama’a cewa za a kula da fashewar bama-baman dan haka kada kada su firgita.

Dahiru Abdulsalam ya kara da cewa ana kara shawartar mutane da su gudanar da harkokinsu na yau da kullum kasancewar babu wani abin damuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: