Shugaba Buhari zai yi taro da manyan hafsoshin tsaron Najeriya domin sake duba halin da tsaro

0 41

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi taro da manyan hafsoshin tsaron ƙasarnan, a yau Litinin domin sake duba halin da tsaron ƙasarnan ke ciki.

A wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasar kan kafafen yada labarai na zamani Bashir Ahmed ya fitar.

Ya ce a lokacin ganawar shugaban ƙasar zai saurari bayanai daga manyan hafsoshin tsaron, tare da bukatar ƙara ƙaimi a fannonin da ke buƙatar kulawar gaggawa.

Kafin hakan dai a Yan kwanakin nan ne dai Ofisoshin jakadancin Amurka da na Birtaniya a Najeriya suka fitar da jerin gargaɗin cewa, akwai barazanar kai hare-hare a wasu sasan ƙasar, har ma da babban birnin tarayya Abuja.

Yayin da suke mayar da martani akan rahotonnin hukumar tsaron farin kaya ta kasa DSS ta bukaci mazauna Abuja akan su kwantar da hankalinsu.

Ana bagaren shugaban kasa Muhammadu Buhari yace ofishin jakadancin Amurka da Birtaniya, basa nufin cewa za’akai hare-hare a Abuja, kawai dai sun bada shawarwari ne.

Leave a Reply

%d bloggers like this: