Shugaba Tinubu da Kashim zasu kashe sama da ₦10.13Bn a matsayin kudin abinci da tafiye-tafiye

0 192

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakin sa Kashim Kashim zasu kashe sama da Naira Bilyan 10.13 a matsayin kudin abinci da tafiye-tafiye, kamar dai yadda kasafin kudin shekarar 2024 ya nuna.

Majalisar dokokin kasar nan nayin nazari kan kudi kimanin Naira Tiriliyan 27.5 na kasafin kudin shekarar mai kamawa.

A cewar kasafin kudin, Shugaba Tinubu zai kashe Naira Milyan dari 638.5 a tafiye-tafiyen cikin gida da kuma Naira Bilyan 6.9 na tafiye-tafiyen kasashen waje, adadin kudin ya kama Naira Bilyan 7.6.

Mataimakin shugaban kasa zai yi amfani da Naira Bilyan 1.8 domin tafiye-tafiye cikin gida, da kuma Naira Bilyan 1.2 na tafiye-tafiyen kasashen ketare.

Sannan an warewa ofishin shugaban kasa da mataimakin sa Naira Milyan dari  660.5 a matsayin kudin abinci, ofishin shugaban kasa zai samu Naira Milyan dari 287.8 daga cikin kudin, yayinda na mataimakin shugaban kasa zai samu Naira Milyan dari 254.2. Daga cikin kudin mataimakin shugaban kasa zai kashe Naira Milyan 35 a matsayin kudin shakatawa da abinci, da karin Naira Milyan dari 337.5 a matsayin kudin kayan abinci da na makulashe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: