Shugaba Tinubu ya nemi gwamnonin jihohi da su yi watsi da sabanin siyasa su hada kai wajen gina kasa
Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi kira ga gwamnonin jihohi da su yi watsi da sabanin siyasa su hada kai da gwamnatin tarayya wajen gina kasa.
Tinubu ya yi wannan kiran ne a lokacin buda baki tare da gwamnoni a fadar gwamnati da ke Abuja, a jiya Alhamis.
Ya kuma jaddada muhimmancin a jiye siyasa a gefe a fuskanci shugabanci, inda ya ce akwai bukatar hadin kai kai a tsakanin masu ruwa da tsaki.
Da yake karin haske kan muhimmancin watan Ramadan Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da lokutan wajen yin addu’o’i, da kuma sadaka.
Shugaban ya bayyana kwarin guiwar samun mafita mai dorewa a nan gaba, inda ya ce gwamnatin sa na iya bakin kokartinta wajen shawo kalubalen da kasar nan ke fuskanta. Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, Shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya kuma Gwamnan Jihar Kwara, ya yabawa gwamnatin tarayya bisa bayarda umurnin raba hatsi da ya kai tan 42,000.