Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sakin Naira biliyan 493 don tallafawa gidaje miliyan biyar a fadin Najeriya, bayan cire takunkumi daga asusun Hukumar Shirin Zuba Jarin Jin Kai ta Ƙasa (NSIPA). Wannan na zuwa ne bayan binciken da aka fara kan ma’aikatar Harkokin Jin Kai tun Janairu 2024, wanda ya haifar da dakatar da Minista Dr Betta Edu da kuma duba tsarin kuɗin shirye-shiryen jin kai.
Karamin Minista Dr Yusuf Sununu ya ce sama da Naira biliyan 500 aka ware don shirye-shirye kamar Shirin Ciyar da Dalibai a Makarantu, Ba da Kuɗi ga Talakawa, N-Power, da Tallafin Manoma. NSIPA za ta fara aiwatar da Shirin GEEP da Grant for Vulnerable Groups, tare da ɗaukar kamfanoni 53 don sabunta bayanan NIN da BVN na masu buƙata domin samun damar tallafin cikin gaggawa.