Shugaba Tinubu ya yi alƙawarin hukunta mutanen da ke da hannu a kisan sojoji 14

0 239

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi alƙawarin hukunta mutanen da ke da hannu a kisan sojoji 14 ranar 14 ga watan Maris a jihar Delta da ke kudancin ƙasar.

Manyan jami’an soji huɗu da sojoji 12 aka kashe a lokacin da suke aikin wanzar da zaman lafiya bayan rikicin da ya faru a yankin Okuama da ke ƙaramar hukumar Ughelli a jihar Delta.

Shugaba Tinubu yace Hedikwatar tsaro da babban hafsan sojin ƙasa na ƙasar nan sun samu amincewa ta hukunta duk wanda aka samu da hannu a mummunan aika-aikar da aka yi kan al’ummar Najeriya Tinubu ya yi magana ne sa’oi bayan da kafafen yaɗa labarai suka ruwaito cewa wasu ɓata-gari sun cinna wuta kan gidaje da dama a yankin na Okuama yayin da mazauna wurin suka tsere saboda fargabar harin ramuwar gayya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: