Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana matukar nadamarsa ga halin da ‘yan Najeriya ke ciki na rashin man fetur da wutar lantarki

0 74

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana matukar nadamarsa ga halin da ‘yan kasarnan ke ciki, sakamakon karancin man fetur da wutar lantarki da aka dade ana fama.

A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya fitar jiya a Abuja, shugaban kasar ya yi imanin cewa batun karancin man fetur matsala ce da gwamnatinsa ta yi nasarar kawar da ita cikin shekaru bakwai da ta yi tana mulki.

Shugaban kasar wanda ya nemi afuwar daukacin ‘yan kasarnan kan karancin man fetur da wutar lantarki a fadin kasarnan, ya kuma bayar da tabbacin cewa nan ba da dadewa ba za a kawo karshen kalubalen.

Shugaban kasar ya nuna bacin ransa kan yadda aka samu rahotannin aikata ba dai dai ba, a gidajen ajiyar man kasarnan.

A saboda haka ya umurci Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur, Hukumar Kula da Man Fetur da Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) da daukacin jami’an tsaron kasarnan da su dauki kwakkwaran mataki kan wadanda ke da hannu wajen aikata wannan ta’asa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: