gwamnatin tarayya tace akwai karin wasu matsaloli da suka jawo daukewar wutar lantarki a kasarnan baki daya, baya ga matsalar raguwar ruwa a madatsun ruwa.

Ministan wutar lantarki, Injiniya Abubakar Aliyu, ya fadi haka a yau lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labaran fadar shugaban kasa bayan zaman ganawar majalisar zartarwa ta tarayya, wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ya jagoranta a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Yana bayar da amsa akan abubuwan da ka iya jawo tabarbarewar samar da wutar lantarki a fadin kasarnan.

Ministan, wanda yace tuni aka fara shawo kan matsalolin, ya bayyana cewa an gyara rushewar tsarin wutar lantarki a fadin kasarnan.

Ya lissafa matsalolin da suka taimaka wajen rashin wutar lantarki a kasarnan da suka hada da rushewar tsarin wutar lantarki da aikin gyara kayan aiki da lalata bututun mai da iskar gas da kuma rikice-rikicen da ake fuskanta wajen samun gas.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: