Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin sa ta jajirce wajen sake fadada hanyoyin karbar haraji a Najeriya

0 98

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin sa ta jajirce wajen sake fadada hanyoyin karbar haraji a kasar nan.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a jiya Talata a taron farfado da hanyoyin karbar kudaden Rabanu a Abuja.

Kakakin Shugaban Kasa Mista Femi Adesina, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, inda ya ce Shugaba Buhari ya bayyana damuwa bisa yadda ake karbar kudaden rabanun wanda suka hada da tsallaken biya da kuma rashin bibiyar kudaden akan lokaci.

Haka kuma ya ce rashin mayar da hankali wajen karbar kudaden rabanun cikin kwarewa da kuma rashin gogewar aiki na daga cikin dalilan da suke kawowa tsaiko.

Muhammadu Buhari, ya ce bukaci a sake ninka kokarin wajen karbar kudaden Rabanun kamar yadda ya ke cikin dokokin karbar Rabanu na kasa.

Haka kuma, ya ce Gwamnatin tarayya baza ta kara yawan kudaden rabanun akan yan kasa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: