Shugaban kungiyar ASUU ya ce nan ba da jimawa za su koma azuzuwa domin ci gaba da koyarwa

0 89

Shugaban kungiyar malaman jami’o’i ta kasa, ASUU, Farfesa Victor Emmanuel Osodekeya ce nan ba da jimawa za su koma azuzuwa domin ci gaba da koyarwa.

Ya bayyana haka ne yayin da ya gana da kakakin majalisar wakila ta kasa, Femi Gbajabiamila a jiya Litinin.

Farfesa Osodeke ya yaba wa matakin da majalisar wakilan kasarnan ta dauka na tsoma baki domin ganin an yi sulhu tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar ASUU wadda ta kwashe wata takwas tana yajin aiki.

Wani bidiyo da aka wallafa a shafin Tuwita na majalisar wakilan Najeriya ya nuna Farfesa Osodeke yana cewa sun kusa kawo karshen yajin aikin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: