Akalla jami’an ‘yan sanda 389 ne suka mutu wajen yaki da Yan kungiyyar Boko Haram a jihar Borno cikin shekaru 11 da suka gabata

0 74

Akalla jami’an ‘yan sanda 389 ne suka mutu wajen yaki da Yan kungiyyar Boko Haram a jihar Borno cikin shekaru 11 da suka gabata.

Da yake jawabi yayin kaddamar da sabon Ofishin Yan sanda da Barikin da aka gina a Beneshiek hedikwatar karamar hukumar Kaga ta jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Borno, Abdu Umar, ya ce an jikkata jami’an Yan sanda 450 cikin shekara 11.

A cewar kwamishinan ‘yan sandan, ankona Barikokin ‘yan sanda 24 da Tashoshi 30 yayin da Yan Boko Haram suka yi awon gaba da kayan aiki da dama.

Umar ya kuma yabawa kokarin Gwamna Babagana Zulum na sake gina wasu Ofisoshin ‘Yan sanda da aka lalata a fadin jihar.

Jihar Borno dai na daya daga cikin jihohin arewa maso gabas da suka fi fama da matsalar tashe tashen hankulan Boko Haram da aka kwashe sama da shekaru 10 ana gwabzawa.

Wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da raba wasu da muhallansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: