Shugaban rukunin kamfanonin BUA ya samar da motoci 25 ga hukumar NDLEA

0 312

Gidauniyar Abdul Samad Rabiu ta Afrika a jiya ta bada gudunmawar motoci 25 ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA domin habaka ayyukan su a Najeriya.

Gundumawar na a matsayin wani mataki domin taimakawa hukumar wajen samar da tsaro a kasar nan, tare da inganta ayyukan ta.

Manajin darakta na gidauniyar Ubon Udoh, wanda ya mika takardu da mukullan motocin ga shugaban hukumar NDLEA Buba Marwa yace, shugaban kamfanin rukunin BUA Abdul Samad ya samar da wannan motocin ne domin daga darajar da inganta mutanen Afrika.

Ya ce motocin zasu taimakawa hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi wajen gudanar da aikin ta yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Da yake maida martani, shugaban hukuma ta NDLEA Buba Marwa ya yabawa gidauniyar bisa bada wannan gudunmawa ga hukumar.

Ya kuma bada tabbacin za’a yi amfani motocin bisa manufar da aka samar da su. Daga bisa Buba Marwa ya mika motocin ga kwamandodin hukumar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: