Shugabannin kungiyar kwadago za su gana da wata tawaga ta shugaba kasa Bola Tinubu

0 595

Shugabannin kungiyar kwadago ta kasa NLC da takwarar su ta TUC sun shirya ganawa da wata tawaga ta shugaba kasa Bola Ahmed Tinubu yau.

Shugaban kungiyar na kasa Joe Ajaero shine ya bayyana haka jiya ga memana labarai.

Mista Ajaero yace sun yanje zanga-zangar da suke yi ne biyo bayan shiga tsakani da majalisar dattawa da kuma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu suka yi, ya kuma kara da cewa daga wancan lokaci kawo yanzu matsala daya zuwa biyu aka tattauna aka.

Ya ce, majalisar dattawan ta kuma alkawarin cewa zata wai-waice su da kuma magance matsalolin da yasa suke zanga-zangar nan da mako guda.

Gidan radio ya rawaito cewa a ranar larabar data gabata ne, Kungiyar kwadago ta kasa NLC da TUC suka jagoranci ma’aikata wajen gudanar da zanga-zanga a fadin kasar nan dangane da tsananin rayuwa da aka shiga biyo bayan sabbin manufofin gwamnati, musamman na janaye tallafin man fetur.

Leave a Reply

%d bloggers like this: