Shugaban Venezuela Nicolás Maduro Ya Ziyarci Brazil A Karon Farko Tun Bayan Da Jair Bolsonaro Ya Dakatar Da Shi A Shekarar 2019

0 62

Shugaban Venezuela Nicolás Maduro ya ziyarci Brazil a karon farko tun bayan da tsohon shugaban kasa mai ra’ayin rikau Jair Bolsonaro ya dakatar da shi a shekarar 2019.
Sabon shugaban kasar Luiz Inacio Lula da Silva ne ya tarbi Nicolás Maduro, gabanin taron shugabannin kasashen Latin Amurka a Brasilia.
Kasashe da dama sun nuna shakku kan sahihancin shugabancin Nicolas Maduro, wanda ‘yan adawa ke bayyana shi a matsayin dan kama-karya.
Da yake gaisawa da bakon nasa a jiya a babban birnin Brazil, shugaba Lula ya ce shima dawowar tasa ta zo ne watanni biyar da suka gabata.
Yana mai nuni da lokacin da ya sake karbar ragamar mulki bayan ya kayar da Jair Bolsonaro a zaben shugaban kasa.
Shugaba Maduro ya kai ziyara ta karshe zuwa Brazil a shekara ta 2015.
Jair Bolsonaro ya kasance mai adawa da shugaban Venezuela mai ra’ayin rikau kuma da wuya ya aika masa da goron gayyata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: