Kamfanin NNPC Ya Kara Farashin Man Fetur Daga Naira 194 Zuwa Naira 537 Kowace Lita

0 103

Kamfanin man fetur na kasa NNPC a yau ya kara farashin man fetur a gidajen sayar da man na kamfanin, bisa la’akari da yanayin da ake ciki na kasuwa a yanzu.
Karin kudin man da kamfanin na NNPC yayi yazo ne sanadiyyar sanarwar da Shugaban Kasa Bola Tinubu yayi na cewa tallafin mai ya kare bayan zuwan gwamnatinsa.
Wakilin kamfanin dillancin labarai na kasa wanda ya bibiyi gidajen sayar da man na NNPC dake Abuja ya bayar da rahoton cewa farashin ya tashi daga naira 194 zuwa naira 537 kowace lita.
Wata sanarwa daga shugaban sashen sadarwa na kamfanin NNPC, Garba Muhammad, tace kasancewar kamfani na cigaba da kokarin samar da ingattacen aikin da aka san shi akai, farashin man zai cigaba da sauyawa bisa yadda kasuwa ta nuna.
Ya godewa yadda abokan huldar kamfanin ke cigaba da mu’amala da kamfanin da ba shi goyon baya da kuma fahimtar juna a wannan lokacin na sauyi da cigaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: