Gwamnatin Tarayya Za Ta Gana Da Shugabannin Kungiyar Kwadago Ta Kasa, Akan Shirin Cire Tallafin Man Fetur

0 84

Gwamnatin tarayya za ta gana da shugabannin kungiyar kwadago ta kasa, NLC, akan shirin cire tallafin man fetur.
Shugaban kungiyar NLC na kasa, Joe Ajaero, wanda ya sanar da haka yayin da ake fira da shi a gidan talabijin na Channels, yace za a gudanar da zaman ganawar a yau.
Yayi bayanin cewa ko da aniyar shugaban kasar ta cire tallafin man mai kyau ce, dole ne a samar da mafita.
Joe Ajaero yace kamata yayi shugaban kasar yayi tambayoyi tare da neman sanin matsalolin da za su faru dangane da cire tallafin man akan ‘yan Najeriyar dake kan tituna.
Shugaban na NLC ya lissafa hanyoyin da za abi domin samun mafita da suka hada da gyaran matatun man kasarnan guda hudu, da samar da sabbin hanyoyin sufuri domin ma’aikatan Najeriya, da sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: