Kimanin Mutane 40 Ne Aka Kashe A Wasu Hare-hare Biyu Da Ake Zargin Masu Ikirarin Jihadi Ne Suka Kai A Burkina Faso

0 87

Rahotanni daga Burkina Faso na cewa kimanin mutane 40 ne aka kashe a wasu hare-hare biyu da ake zargin masu ikirarin jihadi ne suka kai a karshen mako.
Kimanin sojojin sa kai 20 ne suka mutu a kusa da Bourasso kusa da kan iyakar Mali ranar Asabar.
Irin wannan adadin mutane sun mutu a wani harin da aka kai a yankin a ranar Lahadi.
Firaministan Burkina Faso Apollinaire Kyélem de Tambela ya shaidawa majalisar dokokin kasar cewa gwamnatinsa ba za ta taba tattaunawa da masu ikirarin jihadi ba.
A wani lamari mai ban tausayi, mutane goma sha uku ne suka mutu a cikin kwanaki uku, wasu hudu kuma na kwance a asibiti cikin mawuyacin hali bayan cin abinci da ake zargin mai guba ne a kasar Namibiya.
Kafofin yada labaran kasar sun ruwaito cewa dukkan mutanen sun fito ne daga wani gida mai mutane 22 a kauyen Kayova da ke arewa maso gabashin yankin Kavango.
Yawancin wadanda suka mutu yara ne kuma an ruwaito cewa suna cikin tsananin bukatar abinci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: