Kungiyar Kwadago Ta Kasa, NLC, Ta Bukaci Kamfanin NNPC Ya Janye Samfurin Farashin Man Fetur Da Aka Saki

0 87

Kungiyar Kwadago ta Kasa, NLC, ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta umurtar kamfanin man fetur na kasa, NNPC Limited, da ya janye samfurin farashin man fetur da aka saki domin samun damar tattaunawa a tsakanin bangarorin.

Shugaban kungiyar ta NLC, Joe Ajaero ne ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu, kuma ya rabawa manema labarai jiya a Abuja.

Joe Ajaero ya ce sabon samfurin farashin abu ne mai tayar da hankali mai cike da matsaloli kuma yana iya kawo cikas ga tattaunawar da kungiyar ke yi da gwamnatin tarayya.

Ya kara da cewa abin da gwamnati ta yi shi ne dora bindiga a kan al’ummar Najeriya da kuma matsin lamba ga shugabanni, wanda hakan ke kawo cikas ga tattaunawar.

Shugaban na NLC ya ce ‘yan Najeriya ba za su amince da duk wata rufa-rufa daga kowane bangare ba, musamman daga wakilan gwamnati.

Leave a Reply

%d bloggers like this: