Gwamna Umar Namadi Ya Kafa Kwamitin Sa Ido Akan Farashi Da Rarraba Man Fetur A Jihar

0 93

Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya amince da kafa kwamitin mutane 12 a kan sa ido akan farashi da rarraba man fetur a jihar.

Shugaban ma’aikata na jiha Alhaji Hussaini Ali Kila a wata sanarwa da ya fitar a Dutse ya ce an nada Kanar Muhammad Alhassan mai ritaya a matsayin shugaban kwamitin.

Hussaini Kila ya ce kwamitin zai tabbatar da wadatar man da kuma rarraba albarkatun man fetur a fadin jihar.

Mambobin kwamitin sun hada da Muhammad Usman Na-Allah, wakilan ma’aikatar kasuwanci da masana’antu da ma’aikatar yada labarai, matasa, wasanni da al’adu. Sauran sun hada da wakilan rundunar ‘yan sandan Najeriya, da na hukumar tsaro ta farin kaya DSS, da na sojojin Najeriya da na hukumar tsaron fararen hula civil defence, da yan kasuwar man fetur masu zaman kansu, da sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: