Hukumar NSCDC A Jigawa Ta Kama Wani Mutum Mai Shekaru 67 Bisa Zargin Yin Lalata Da Yarsa

0 110

Hukumar tsaron fararen hula civil defence reshen jihar Jigawa ta kama wani mutum mai suna Musa Garba mai shekaru 67 bisa zargin yin lalata da ‘yarsa Ummi Garba mai shekaru 25 da haihuwa.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa ya ruwaito cewa an kama Musa Garba ne tare da matarsa Aisha Garba mai shekaru 50 a unguwar Tukur da ke karamar hukumar Dutse a jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar na jiha, Adamu Shehu, ya rabawa manema labarai jiya a Dutse.

Adamu Shehu ya ce kamen ya biyo bayan rahoton wani da ake zargi da cin zarafin wani mutum, da wani mai rajin kare hakkin dan Adam ya shigar gaban hukumar a ranar 26 ga watan Mayu. Adamu Shehu ya ce wanda ake zargin ya gabatar da katin asibiti da ya samu a shekarun 2013, 2014 da 2018 daga asibitin masu tabin hankali da ke Kazaure, inda yaje domin a warkar da shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: