Wata Kungiyar Farar Hula Ta Bukaci EFCC Ta Kama Tsohon Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje

0 83

Wata kungiyar farar hula mai yaki da rashin adalci ta bukaci hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC da ta kama tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje tare da gurfanar da shi a gaban kotu bisa faifan bidiyo da aka gan shi yana karbar cin hanci daga hannun ‘yan kwangila.

A watan Oktoban 2018, jaridar Daily Nigerian ta wallafa bidiyo na musamman da ke nuna gwamnan jihar Kano na wancan lokacin yana cusa makudan kudaden dala a aljihunsa da ake kyautata zaton ’yan kwangila ne suka bashi cin hanci.

A wata wasika mai dauke da kwanan watan 31 ga watan Mayu, da aka aika zuwa ga kwamandan hukumar EFCC na shiyyar Kano, kuma aka yi kwafinta zuwa ga hukumar ICPC, babban daraktan kungiyar, Ibrahim Umar, ya bukaci hukumomin na yaki da cin hanci da rashawa da su sake bude binciken tunda gwamnan ya rasa rigarsa ta kariya daga shari’ah. Kungiyar ta tunatar da yadda majalisar dokokin jihar Kano ta fara gudanar da bincike kan wannan zargi amma an dakatar da ita bayan hukuncin da wata babbar kotun jihar Kano ta yanke.

Leave a Reply

%d bloggers like this: