Akalla Mutane 17 Ne Suka Mutu Yayin Da Wasu 106 Suka Jikkata Jiya A Kudancin Khartoum Na Kasar Sudan

0 88

Akalla mutane 17 ne suka mutu yayin da wasu 106 suka jikkata a jiya bayan da wasu rokoki suka fada kan wata kasuwa a kudancin Khartoum babban birnin kasar.

Wannan shi ne adadi mafi yawa na mutane da aka kashe ta hanyar luguden wuta a wani hari da aka kai a kusa da babban birnin kasar tun bayan fadan da aka gwabza tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF a ranar 15 ga Afrilu.

Harin dai ya zo ne a daidai lokacin da tattaunawar da kasashen Amurka da Saudiyya suka kulla domin kawo karshen rikicin ta ruguje.

Harin ya kara adadin fararen hula da suka mutu a rikicin zuwa 883.

A wani labarin kuma daga Afirka, wata kotu a kasar Senegal za ta sanar da yanke hukunci nan gaba kadan a shari’ar zargin fyade da ake yi wa madugun ‘yan adawa, Ousmane Sonko.

Babban birnin kasar, Dakar, ya kasance cikin shirin fuskantar tashin hankali. Magoya bayan dan siyasar dai sun ce an kitsa wannan lamari da nufin hana Ousmane Sonko tsayawa takara shugaban kasa a zaben shekara mai zuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: