Najeriya Ta Fitar Da Argentina Daga Gasar Cin Kofin Duniya Na ‘Yan Kasa Da Shekaru 20

0 106

Najeriya ta fitar da Argentina mai masaukin baki bayan kwallayen da Ibrahim Muhammad da Rilwanu Haliru Sarki suka ci inda suka fitar da zakarun gasar sau shida a gasar cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekaru 20 a jiya.

Kungiyar ta Flying Eagles ta taka rawa gani domin tsare gidanta, daga nan suka zura kwallaye biyu ta hanyar kai hari cikin sauri.

Kocin ‘yan wasan na Najeriya Ladan Bosso ya yi alkawarin cewa yaransa za su yi kokari sosai, kuma sun yi hakan har ma fiye da yadda ake tsammani a filin wasan.

A wani labarin makamancin wannan, kungiyar kwallon kafa ta mata ‘yan kasa da shekaru 20 ta Najeriya, Falconets, za ta kara da takwararta ta Ghana a wasan karshe na gasar cin kofin ‘yan kasa da shekaru 20 na Kungiyar Kwallon Kafa ta Afrika ta Yamma a ranar Asabar. Najeriya ta lallasa Jamhuriyar Benin da ci 3 a wasan daf da na karshe a gasar a jiya inda za su fafata da mai masaukin baki Ghana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: