Hukumar EFCC Na Binciken Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi

0 74

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta maka tsohon gwamnan Ekiti, Dr Kayode Fayemi, kan zargin karkatar da kudi da kuma karkatar da naira biliyan hudu.

Wata majiya da ke kusa da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta bayyana cewa Kayode Fayemi ya isa harabar hukumar EFCC da misalin karfe 10 na safiyar jiya kuma jami’an hukumar ne suka rako shi.

Majiyar ta ce tsohon gwamnan yana ofishin shiyya na hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a Oko Close a Ilorin a jihar Kwara domin yi masa tambayoyi kan zargin zamba.

A cewar majiyar, EFCC na yiwa tsohon gwamnan tambayoyi kan zargin karkatar da naira biliyan 4.

Binciken dai an ce yana da nasaba ne da yadda ya tafiyar da kudade a lokacin da yake gwamnan jihar Ekiti.

Kayode Fayemi ya kasance gwamnan jihar daga 2018 zuwa 2022 kuma ya mikawa Gwamna Biodun Oyebanji mulki a watan Yunin 2022.

Leave a Reply

%d bloggers like this: