Shugabar tawagar aikin AcReSAL ta Bankin Duniya, Dr Joy Agene, ta jinjinawa Gwamnatin jahar jigawa

0 123

A wata ziyara ta musamman da ta kai jihar Jigawa, shugabar tawagar aikin AcReSAL ta Bankin Duniya, Dr Joy Agene, ta jinjinawa Gwamnatin Jigawa bisa gaskiya da rikon amana wajen aiwatar da ayyukan dorewa

Agene ta bayyana hakan ne lokacin da ta kai wa Gwamna Umar Namadi ziyarar ban girma a Dutse, inda ta yaba da yadda gwamnatin ke gudanar da aiki cikin gaskiya da tsari, tana mai cewa Jigawa na daya daga cikin jihohin da suka fi kowa aiki tukuru a fadin kasar nan.

Ta ce ko da suna taro da sauran jihohi, Jigawa na bayyana a matsayin abin koyi saboda hadin gwiwar bangarori daban-daban da kuma kokarin gwamnatin wajen tabbatar da an kai ayyukan ga al’umma.

A nasa bangaren, Gwamna Namadi ya yi godiya da yabo da kuma tabbatar da cewa aikin AcReSAL ya taimaka matuka wajen magance matsalolin ruwa, zaizayar kasa, da saharar da ke barazana ga yankin.

Leave a Reply