Sojojin Najeriya da ‘yan banga sun ceto mutane 6 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su

0 207

Dakarun sojojin Najeriya da ‘yan banga sun ceto wasu mutane shida da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a dajin dake karamar hukumar Shanga a jihar Kebbi.

Mutanen da aka yi garkuwa da su, an ce to su ne cikin koshin lafiya a ranar Juma’ar data gabata kuma tuni aka mikasu   ga iyalansu.

Wannan dai na kunshe cikin wata sanarwa da mai baiwa gwamna  Nasir Idris na jihar Kebbi shawara kan harkokin yada labarai Malam Yahaya Sarki ya fitar a jiya.

Sanarwar tace jami’an tsaro a yankin da suka hada da sojoji da ’yan banga, sun shiga cikin dajin Shanga, inda jami’an tsaron suka yi nasarar ceto wadanda aka yi garkuwa da su. Ya kuma yaba da irin namijin kokarin da sojojin ke yi, inda ya jaddada kudirin gwamnatin Kauran Gwandu na tallafawa hukumomin tsaro a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: