Gwamnatin jihar Kwara ta bayyana shirinta na kawar da bahaya a bainar jama’a a fadin jihar

0 139

Gwamnatin jihar Kwara ta bayyana shirinta na hada kai da duk wata hukumar dake bada tallafi domin kawar da bahaya a bainar jama’a a jihar.

Kwamishinan Albarkatun Ruwa na jihar Yunusa Lade, shine ya bada wannan tabbacin lokacin da wata tawagar asusun bada agajin gaggawa ta Majalisar Dinkin Duniya karkashin jagorancin Misis Theressa Pammer ta ziyarci ofishinsa dake Ilorin babban birnin jihar.

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta ware kudi naira Miliyan 200 domin samar da bandakuna da sauran abubuwan da za su hana yin bahaya a bainar jama’a. Ya ce ‘yan majalisar, a matakin jiha da na tarayya sun dukufa wajen ganin sun kara kaimi a kokarin da gwamnatin jihar keyi na kawar da dabi’ar bahaya a bainar jama’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: