Gwamnan jihar Sokoto ya bayar da umarnin sake gyara gidan marigayi Shehu Shagari da gobara ta kone

0 145

Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, ya bayar da umarnin sake gyara gidan marigayi tsohon shugaban kasa Shehu Shagari da gobara ta kone a makon jiya.

Gwamnan ya bada umarnin ne ranar Asabar jim kadan bayan ya ziyarci gidan tsohon shugaban kasar da ya kone domin tantance irin barnar da gobarar tayi.

Ya bayyana gobarar a matsayin ibtila’i, inda ya ce gidan da ya kone ya kasance gidan tarihi ba wai ga jihar Sakkwato kadai ba har ma da kasa baki daya.

Yayin da yake jajantawa iyalan marigayi tsohon shugaban kasar kan wannan gobara, gwamna Aliyu yayi addu’r Allah madaukakin Sarki da kiyaye afkuwar hakan a nan gaba. Gidan rediyon Sawaba ya ruwaito cewa, gobara ta kone gidan tsohon shugaban kasa marigayi Shehu Shagari a makon da ya gabata, wanda hakan ya yi sanadiyyar asarar dumbun dukiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: