Gwamnatin mu na yunkurin baiwa jami’o’in kasar nan cikakken ‘yancin cin gashin kai

0 229

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatin sa na kokarin bullo da manufar da za ta baiwa jami’o’in kasar nan cikakken ‘yancin cin gashin kai.

Shugaba Tinubu wanda ya samu wakilcin ministan harkokin Neja Delta, Engr. Abubakar Momoh ya bayyana haka a garin Benin a karshen mako da ya gabata yayin taron karo na 48 na jami’ar Benin.

Ya ce yana da yakinin cewa ‘yancin cin gashin kan jami’o’i zai inganta fannin ilimin jami’o’i.

Momoh ya ce gwamnati mai ci ta yi imanin cewa wannan mataki ne da ya dace. Shugaban kasar ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen sake farfado da harkar manyan makarantu da kuma fannin ilimi domin samar da sakamako mai kyau.

Leave a Reply

%d bloggers like this: