Gwamnatin tarayya ta gargadi manoma kan sayarwa ko karkatar da kayayyakin noman rani da aka basu

0 239

Gwamnatin tarayya ta gargadi manoma kan sayarwa ko karkatar da kayayyakin noman rani na shekarar 2023 da aka basu.

Ministan noma da samar da abinci Sanata Abubakar Kyari shine ya yi wannan kiran a taron kaddamar da shirin noman rani na shekarar 2023 karkashin shirin bunkasa noma na kasa a jihar Jigawa.

Sanata Kyari ya ce gwamnati mai ci ta kudiri aniyar karfafa gwiwar manoma domin su noma kayan abinci irin su shinkafa, masara, rogo da alkama, a fadin kasar nan.

A cewarsa, manoma suna samum isasshen tallafi da kashi 50 cikin dari na tallafin kayan noma da nufin rage hauhawar farashin kayayyaki, da kuma dogaro da  kayan da ake samarwa a Najeriya, tare da kara yawan abubuwan da ake samarwa a cikin gida.

Ya bukaci manoman da su yi amfani da tallafin domin cimma burin da aka sa a gaba. Ministan ya umurci hukumar tsaro ta farin kaya ta civil defence da sauran hukumomin tsaro da su sanya ido a kan yadda ake rarraba kayayyakin domin kaucewa karkatar da kayan noman da aka baiwa manoman.

Leave a Reply

%d bloggers like this: