Sojojin Najeriya, sun kama wasu mutane biyu da ake zargin su dayin garkuwa da mutane a jihar Taraba.
Yayin wannan aikin da sojojin suka yi sun ceto wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su a yankin babban bankin Najeriya, CBN, dake Jalingo, babban birnin jihar.
Kwamandan Birgediya Janar Frank Etim ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau litinin.
A cewarsa, an gudanar da aikin ne da sanyin safiyar jiya Lahadi biyo bayan samun sahihan bayanai game da ayyukan ‘yan ta’adda a cikin babban birnin jihar. Ya kara da cewa sauran wadanda ake zargin sun yi nasarar tserewa bayan ganin sojojin dake shiga yankin, kwamandan ya kara da cewa “ana kokarin kama su domin fuskantar hukunci.