Ko kadan gwamnatina ba ta adawa da sanya hijabi daga bangaren mata musulmi – Mohammed Bago

0 215

Gwamnan jihar Neja, Mohammed Bago, ya ce ko kadan jihar ba ta adawa da sanya hijabi daga bangaren mata musulmi.

Muhammad Bago ya mayar da martani ne kan wani rahoto da aka wallafa a kafafen sada zumunta dake ikirarin cewa kwamishiniyar ilimi ta jihar, Hajiya Hadiza, ta yi Allah-wadai da sanya hijabi da Malamai mata ke yi.

Rahoton ya zargi kwamishiniyar da cewa sanya hijabi ga Malamai mata zai hana su yin abun da ya kamata yayin koyarwa.

Gwamnan, a wata sanarwa da ya fitar jiya ta hannun babban sakataren yada labaransa, Bologi Ibrahim, ya ci gaba da cewa gwamnatin sa bata da hurumin hana sanya hijabi, domin hakan abu ne da ya shafi doka ta addini. Gwamnan ya ce, zargi ne kawai aka yiwa kwamishiniyar  kasancewar gwamnatin jihar Neja na goyon bayan yadda mata ke amfani da hijabi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: