‘Yan sanda a Kasar Austireliya sun kama masu gudanar da wata zanga-zangar sauyin yanayi

0 287

‘Yan sanda a Kasar Austireliya a yau Litinin sun kama sama da masu fafutukar sauyin yanayi 100 bayan da suka gudanar da wata zanga-zanga a wata tashar ruwa mafi girma a kasar.

Masu fafutukar da aka kama a cewar ‘yan sanda sun hada da yara biyar da wani mai shekaru 97.

Tawagar sun toshe zirga-zirgar jiragen ruwa a karshen mako a tashar jiragen ruwa ta Newcastle da ke gabar tekun gabashin Austireliya, suna rokon gwamnati da ta kawo karshen dogaron da kasar ta yi kan fitar da mai.

Hukumomin kasar sun amince da barin zanga-zangar na tsawon sa’o’i 30, amma kwale-kwalen ‘yan sanda sun fara korar masu zanga zangar a cikin ruwan dai-dai lokacin da wa’adin da aka basu ya cika amma masu fafutukar suka yi biris da ficewa daga cikin ruwan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: