Spain Ta Rufe Sararin Samaniyarta Ga Jiragen Yaƙin Amurka da Suka Kai Wa Iran Hari

0 126

Ministan tsaron ƙasar Sipaniya, Margarita Robles ta ce ƙasar ta rufe sararin samaniyyarta ga jiragen yaƙin Amurka da suka kai hare-hare kan Iran.

“Ba za mu bari an yi amfani da sansanin sojin Moron and Rota domin aikata duk wani abu mai alaƙa da yaƙar Iran ba,” in ji ta inda ta ƙara da cewa Sipaniya ta “fayyace wa gwamnatin Amurka matsayarta tunda fari.”

Ministan harkokin wajen ƙasar, Jose Manuel Albares ya ce manufar ɗaukar matakin ita ce “ka da a yi duk wani abun da zai iya rura wutar yaƙin.”

Wani jami’an fadar White House ta Amurka ya shaida wa BBC cewa sojojin Amurka na “samun nasara ko ma sun wuce nasarar da ake son cimma a yakin saboda haka Amurka ba ta buƙatar taimakon Sipaniya ko waninta.”

A baya dai Donald Trump ya yi barazanar ƙaƙaba wa Sipaniya takunkumi bisa ƙin adawar da take da yaƙar Iran.

Leave a Reply