Shugaban hukumar kula da cutar HIV ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi gargaɗin cewa matakin da Amurka ta ɗauka na janye ɗaukacin tallafin da take bayarwa kan cutar HIV a Afirka ta Kudu na iya haifar da asarar rayuka.
Shugabar UNAids Winnie Byanyima ta shaida wa manema labarai gabanin taron Majalisar Dinkin Duniya kan cutar, cewa matakin na Amurka na iya jefa waɗanda ke ɗuek da cutar cikin mawuyacin hali.
Afirka ta Kudu ba ta dogara kan tallafin da Amurka ke ba wa ta fannin magungunan cutar ba, amma Amurka ta ba da gudummawa sosai ga shirye-shiryen ƙasar na hana yaɗuwarta.
Jami’an Amurka sun shaida wa BBC cewa rage tallafin wani ɓangare ne martanin Amurka kan rashin kare rayukan al’ummar farar fata da ake zargin gwamnatin Afirka ta Kudu ta gaza.
Zargi da Pretoria ta musanta.
Ma’aikatar lafiya ta Afirka ta Kudu ta mayar da martani da cewa duk da cewa ba a sanar da ita wannan matakin a hukumance ba, amma ta daɗe tana aiki kan shirin dogaro da kai.