Tinubu Da Matarsa Sun Sauka A Kasarnan Yau Litinin Bayan Tsawon Lokaci.

0 77

zababben shugaban kasa mai jiran gado, Bola Tinubu da matarsa, Oluremi Tinubu, sun sauka a kasarnan yau Litinin bayan tsawon lokaci.
Bola Tinubu, wanda ya tafi kasar Faransa tun ranar 21 ga watan Maris, ya sauka da misalin karfe 4 da rabi na yamma a filin jiragen saman Nmandi Azikiwe dake Abuja, kwanaki 35 kafin rantsar da shi.
Zababben shugaban kasar mai jiran gado tare da matarsa sun samu tarba daga zababben mataimakin shugaban kasa mai jiran gado, Kashim Shettima, da gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, da wasu jiga-jiga jam’iyyar APC mai mulki.
Ofishin yada labaran Tinubu a watan Maris ya ce Bola Tinubu yayi tafiyar ne domin ya samu hutu saboda shirin tunkarar bikin rantsar da shi.
Ofishin yace ce zababben shugaban mai jiran gado ya yanke shawarar yin hutu ne bayan yakin neman zabe da lokacin zabe domin hutawa a biranen Paris da Landan, da shirin zuwa Saudiyya domin yin Umrah da kuma Azumin Ramadan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: