Shugaba Buhari Zai Halarci Taron Ƙolin Shugabannin Ƙasashen Yankin Tekun Guinea

0 93

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai halarci taron ƙolin shugabannin ƙasashen yankin tekun Guinea da za a gudanar a gobe talata a Accra babban birnin ƙasar Ghana.
Cikin wani saƙo da fadar shugaban ƙasar ta wallafa a shafinta na Tuwita, ta ce shugaban zai bar Najeriya gobe Talata 25 ga watan Afrilu domin halartar taron, wanda shugaban ƙasar Ghana Nana Akuffo-Ado zai jagoranta.
Ana sa ran shugaban zai gabatar da jawabi a taron wanda zai tattauna dabarun ƙarfafa zaman lafiya da tsaro da yaƙi da masu aikata miyagun laifuka a gaɓar tekun yankunan ƙasashen.
Yayin halartar taron, shugaban zai samu rakiyar ministan harkokin ƙasashen wajen ƙasar Geoffrey Onyeama, da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno mai ritaya, da daraktan hukumar tattara bayanan sirri ta ƙasa Amb. Ahmed Rufai Abubakar, da sauran jami’an gwamnati.

Leave a Reply

%d bloggers like this: